Ana səhifə

Majdi muhammad bin ali bin muhammad


Yüklə 0.54 Mb.
səhifə1/12
tarix12.05.2016
ölçüsü0.54 Mb.
  1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12
RINJAYEN GASKIYA

TATTAUNAWA NA ILIMI DA WASU ‘YAN SHI’A IMAMIYYA

NA

MAJDI MUHAMMAD BIN ALI BIN MUHAMMADMai fassara: ALIYU IBRAHIM ALTUKRI

aitukuri07@yahoo.com

ISBN: 978-8092-68-3SADAUKARWA
Zuwa ga duk wani musulmi, tsaftatacce, tsarkakakke, mai yin riqo da littafin Allah Azza wa Jalla, da sunnar Annabinsa mai karamci (SAW), kuma mai bin tafarkin muminai Sahabban Annabi masu girma da nagarta (RA), kuma mai nuna qauna da soyayya da jivintar dangin Annabi da Iyalan Gidansa tsarkaka masu tsarkakewa, mafificiyar tsira da mafi cikan amincin Allah su tabbata a garesu.

Da fatan wannan (littafi) zai qara masa yin riqo da waxannan jijiyoyin (tushen) da a kan su ne aka gina aqidun vangaren da zai samu tsira kuma jama’ar da zata yi rinjaye wacce take samun taimako, watau Ahlulsunnati.

Da kuma zuwa ga duk wani malami mai tsoron Allah, wanda ya zurfafa a ilimi kuma mai aiki da ilminsa, wanda yake matuqar qoqarinsa wajen yaxa sunnah da yaqan bidi’a da kuma goyon bayan gaskiya da kore qarya.

Da fatan zai sani cewa akwai shi da yan’uwan da suke mara mashi baya wajen taimakon gaskiya da yin toshiya ga ma’abota bidi’a da vata, da mushrikai da kafirai, da zindiqanci da mulhidai.

Da kuma zuwa ga duk wani mai binciken neman tafarkin Allah madaidaiciya a tsakanin hanyoyin qungiyoyin vata.

Domin ya iya rarrabe tsakanin gaskiya da qarya, da shiriya daga vata, da sunnah daga bidi’a, da imani daga kafirci, da tsarkaka daga dauxa, da tsira daga tavewa.

Da kuma zuwa ga duk wani mai kurarin neman haxin kai na coge da neman daidaito na qarya wanda da shi ne mujrimai suke damfaran masu kyautata zato da kyakkyawan niyya.

Domin ya sani cewa babu mahaxa tsakaanin haske da duhu, da tsakanin imani da kafirci, da tsakanin taqawa da mulhidanci.

Haka kuma saboda ya sani cewa shi musulmi na gaskiya ko kusa ba zai karkata zuwa ga azzalumai ko vatattu ba wajen xabbaka umarnin Allah ta’ala wanda Ya ce: “Kada ku karkata zuwa ga waxanda suka yi zalunci har wuta ta shafe ku” (Hud: 113)

GABATARWAR MAI FASSARA

Da sunan Allah Mai Rahmah Mai Jinqai.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya aiko Manzon Sa da shiriya da addinin gaskiya domin ya rinjayar da shi akan dukkan addinai ko da musrikai ba su so. Muna gode masa kuma muna neman taimakon Sa da neman gafarar Sa daga dukkan zunuban mu da munanan ayyukan mu. Tsiran da Amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta kuma mai ceton mu Annabi Muhammad da dukkan Iyalan Gidan sa tsarkaka da kuma ilahirin Sahabban sa zavabbun zavavvu, da kuma waxanda suka bi tafarkin su da kyautatawa har zuwa ranar qiyama.

Bayan haka ina qara bayyana godiya ta ga Allah (SWT) da Ya ba ni dama da ikon kammala wannan aiki na qoqarin fassara wannan littafi mai suna “INTISARU AL HAQ : Munazhiratu al ilmiyyah ma’a ba’adi al- shi’ah al imamiyyah” na Majdi Muhammad Bn Ali Bn Muhammad, zuwa harshen hausa. Haqiqa wannan aiki ne ba mai sauqi ba a gare ni kasancewa xan qaramin xalibi a wannan janibi. Kuma shakka babu a lokacin da na karanta wannan littafi na yi burin a samu wani malami qwa ya jivincin aikin fassaran domin irin alfanun da yake cikin wannan littafin, musamman ga matasa masulmai a wannan vangare da muke ciki na Arewancin Nigeria. To amma hakan bai samu ba. Saboda da haka sai na zage damtse na kuma yi xamaran shiga wannan aiki bisa yardan Allah da kuma dogaro gare Shi. Kuma alhamdu lillahi, bayan tsawan lokaci Allah ya nufe ni da kammalawa.

Babu ko shakka wannan littafi zai yi fa’ida qwarai da gaske wajen warware da’awar makirci da yaudara da zindiqan ‘yan Rafida (shi’a) suke yaxawa a tsakanin al’ummar masulunci a wannan qasar wanda aka sani tsawon zamani suna bin tafarkin tsira ne na Sunnah. Daga sama da shekaru goma da suka wuce zuwa yau, Allah Shi kaxai Ya san irin dubban masulman da aka gurvatawa aqida kuma aka karkatar da su daga ingantattu kuma lafiyayyar imanin su aka dulmuyar da su cikin halakar shi’anci. Kuma da yawa-yawan ire iren waxannan masulman, akasarin su matasa, an samu damar yin galaba a kan su ne da sunan soyayya ga Ahlul Baitin Annabi (SAW) da sauran qarerayi da suke bazawa a cikin al’ummah. Na yi imanin cewa duk wanda ya karanta ainihin littafin da wannan Malami ya rubuta akan muqabalar da ta wakana a tsakanin ‘yan shi’a da Malamin Sunnah, zai samu waraka da yardan Allah. Wanda kuma tun farko bai kamu ba zai samu qarin yaqini tare da samun makaman yaqan gurvatattar aqidar shi’awa.

Na yi iya qoqari na domin in samar da fassarar da ta yi kusa da bayar da ma’anar abin da shi marubucin littafin ya rubuta. Kuma bayan na kammala na nemi sashen ‘yan’uwa masana waxanda na iya kaiwa gare su, domin su duba aikin kuma su yi gyara da tantancewa. Bayan tsawon lokaci hakan bai samu ba saboda irin halin rashin sukuni da suke ciki. A qarshe dai mun yi shawaran buga littafin ne kai tsaye tare da fatan karvan duk wasu gyare gyare da malamai za su tsinkayo a nan gaba.

Muna cike da kyakkyawar fatan Allah, bisa LuxufinSa da RahmarSa, Ya sa wannan littafi ya zama sanadiyan tsamo xinbin matasan da suka shiga ruxu da ximauta har suka faxa tarkon makircin Rafida (Shi’a), suna bi titi titi suna aibata waxanda Allah da kansa Ya tsarkake, Ya kuma yarda da su tare da tanadar masu da Aljannah, watau Sahabban Annabi, Allah Ya qara masu yarda. Da kuma fatan ya zama kangiya ga sauran jama’a musulmai daga faxawa wancan tarkon da sunan wai haxin kai tsakanin Sunnah da Shi’a !! Amin

Aliyu Ibrahim AltukriTammat bi hamdillahi

Ranar Litinin (Karfe 1.07 pm)

10 ga Ramadan, 1430(Hijrah)

GABATARWA
Haqiqa godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maShi, muna neman taimakon Shi, muna neman gafararShi, muna neman tsarin Allah daga sharrorin kawunanmu da munanan ayyukan mu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi kuma wanda aka vatar da shi babu mai shiryar da shi. Ina kuma shaidawa babu wani ilahi sai Allah shi kaxai, ba shi da abokin taraiya; ina kuma shaidawa lallai Muhammad bawan shi ne kuma Manzon shi ne, salati da aminci da albarkan Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da dukkan Sahabban shi. Bayan haka:

Haqiqa magana ya inganta daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Lallai Al-ummar masulunci za ta kasu kashi saba’in da uku, duka suna cikin wuta in banda guda daya”

Kashin da zata tsira itace kashin da ta yi riqo da abin da Annabi (SAW) ya kasance akai, shi da Sahabban shi masu girma da nagarta, shugabannin mummunai kuma jagororin masu taqawa, kuma mafi alherin mutane baya ga Annabawa kuma mafi alherin al’umma wanda aka fitar ga mutane. Allah ta’ala Ya ce: “Kuma wanda ya savawa Manzo daga bayan shiriya ta bayyana a gareshi, kuma ya bi wanin hanyar muminai, zamu jivinta masa abinda ya jivinta, kuma mu qone shi da Jahannama kuma ta munana ta zama makoma” (Al-Nisa’i 115)

Kuma masu aqida da bin koyarwar da qungiya mai rinjaye kuma kashin da zata tsira suke a kai, wato Ahlul Sunnah Wal jama’a, sun tsayu ne a kan yin riqo da Sunnar Annabi (SAW) da bin tafarkin muminai.

Malaman wannan kashin da zata tsira ba su gushe ba suna bayanin tushen vata na sauran kashi saba’in da biyu vatattu waxanda suka cancanci azaba da wuta,kuma daukacin su sun cimma matsaya kuma sun yi itifaqi gaba daya cewa shi’ah ce mafi vata cikin wadancan kashe-kashen, har ma suke kiranta ‘mabiyan qarya’ (shi’atul baxil), ko ‘mabiyan vata’ (shi’atul al dalal), ko mabiyan son zuciya (shi’atul hawa). Su dai waxannan mabiya son zuciya (shi’atul al hawa) su ne mafi vata cikin qungiyoyin masulunci saboda kasancewar su mutane ne da ba su yin anfani da hankali ko nassi, sun kasance kamar dabbobin gida, kai sun ma fi su vacewa.

Kuma abu mafi haxari abin lura a nan shine cewa su shi’atul dalal sun ka su zuwa kashi xari uku da talatin, sannan kuma a cikin su kashin da ta fi vacewa ita ce vangaren Ithna ashariyya. Wannan kuwa saboda ita ba ta bar duk wani nau’in vata ba, tsoho ko sabo, face ta yi riqo da shi, ta gamtse shi daram da mataunai. Sannan ba za ta ga wani tafarki miqaqqe ba ko wata gaskiya a sarari face ta sava masa da gangar.

Kuma ita wannan qungiya halakakkiya, addinin ta ya ginu ne a kan wasu shika shikai da rukunai na tsananin vata, saboda an gina shi ne a kan yin kokwanto gami da Alkur’ani, da yin inkari ga Sunnah, da wuce wuri gami da imamai, da kafirta shugabannin muminai wato Sahaban Annabi mai girma, tare da bin tafarki savanin na su, da yin qarya da munafinci da yaudara ta fakewa da mutu’a don halasta zina, da halasta cin dukiyan mutane, da mutuncin su da jinanen su da sunan yin faxa da adawa a madadin Ahlul Baiti, alhali su ne gaba-gaba wajen sava masu da nuna fushin su ga shiryarwan su.

Amma abin al’ajabi, duk da irin halin da suke cikin na halaka da vata da savo da fajirci da qarya da munafunci, sai ga shi har sun samu dama, shaidan da mataimakan shi na ingizo su domin yin toshiya a tafarkin gaskiya kuma hanya madaidaiciya. Ya na zaburar da su domin bayar da himma da lokaci da dukiyar su domin yaxa bidi’ar su da watsa kafircin su da tallafawa vatar su.

Allah ta ala Yana cewa: “Lalle ne waxanda suka kafirta, suna ciyar da dukiyoyin su domin su kange daga hanyar Allah, to, za su ciyar da ita, sa’anan kuma a rinjaye su. Kuma wadanda suka kafirta zuwa ga Jahannama ake tara su. Domin Allah ya rarrabe mumuna daga mai kyau kuma ya sanya mummunan, sashen sa a kan sashe, sa’annan ya sanya shi a cikin jahannama waxannan su ne masu hasara” (Al-Anfal: 36-37)

Haqiqa al’amarin ya firgita ni da qona mani rai ganin yadda waxannan mutane suke yaudaran wasu masulmai masu kyakykyawar niyya da saukin kai, suna shi’antar da su da sunan qauna da soyayya ga Ahlul Baiti. Waxannan masu sauqin kan a cikin mu ba su fahimci cewar duk wannan da’awar soyayyar ga Ahlul Baiti ba wani abu bane face yaudara ne a qudundune, domin fitar da masulmai daga addinin su da imanin su da masuluncin su, zuwa ga cusa kokonto gami da Alkur’ani, da kafircewa Al-Rahamanu da yin gaba da ma’abuta masulunci na qwarai.

Sau da yawa kishi na da hamasa ta ga addini na ya kan motsa yayin da na ga ma’abuta gaskiya zaune sun shantake daga barin gaskiyan na su, alhali ga waxannan masu watsi da gaskiya (Rafidatul Haq) magoya bayan vata (shi’atul baxil) suna tsayuwar daka a kan vatar su, suna riqe da shi qamqam. Kaico! Mutum babu abinda ya iya sai lahaula da istirja’i!

Kuma na samu kai na, bisa yardar Allah, na kasance misalin wata kibiya wajen yaqan waxannan mutane da kawo cikas ga vatar su, lokacin da wani matashi, Ahlul Sunnah, ya zo mani a kixime ya na cikin ruxu. Dalilin kiximewar shi kuwa saboda shi’ah ta kai masa damqa da kazamtacciyar hannu mai cike da najasa da laifuka da fasadi; sun samu damar auka ma sa saboda jahilci da qaranci sanin sa ga aqidojin Ahlul Sunnah Wal Jama’a, wadda ke a kan tafarkin tsira. Haqiqanin alamarin wadannan miyagu kuma lalatattun mutane sun samu damar yaqan sahihiya kuma lafiyaiyar aqidar wannan matashi ne ta anfani da makirci da yaudara, wani lokaci kuma ta hanyar nuna ma shi mamakon karramawa na fitan hankali da mumunar manufa. Haka kuma sun samu shiga zuciyar sa ta fuskar nuna soyaiya ga Iyalan Gidan Annabi (SAW) tsarkaka, yardan Allah ya tabbata a gare su, har wannan miskinin ya zaci kamar su waxansu mala’ikun rahma ne kuma gwarazan yaxa gaskiya. Amma tun ba’a je da nisa ba suka nuna masa cewa fa dole ne soyayiya (ga Ahlul Baiti) ya haxa da qiyaiya da gaba da zagi da la’ana da cin fuska ga ‘maqiyan’ su. Sai shi wannan miskinin ya zaci cewa maqiya Ahlul Baiti su ne yahudu da nasara da mulhidai, ko ire-iren su, maqiya masulunci. Amma tashin hankali sai lokacin da suka yi masa filla-filla suka faxa masa cewa “maqiya Iyalan Gidan Annabi (SAW) su ne Sahabai, ‘kafirai’, waxanda suka yi ridda ‘zindiqai’ kuma ‘munafukai’!”

To, kuma ga shi wannan bawan Allah ya na karanta Alkur’ani, kuma bisa yaqini ya san cewa lallai Sahabban nan su ne gwarazan yaxa gaskiya waxanda Allah Ya zava su riqe amanar addinin Shi, kuma Ya sa su a matsayin mafificiyar alumma da aka fitar ga mutane. Ya kuma sa su mafiya alherin Sahabban Annabawa da Manzanni. Kuma da’iman ya na karantawa a cikin Alkur’ani cewa suna tare da yarda da kyawawan yabo daga Allah. Ya kuma dubi yadda Allah Ya ke kiran su masu taqawa, masu kyautatawa, muminai, mujahidai, masu hakuri da dauriya, masu godiya, ai sai kawai kansa ya buga ya shiga cikin ruxu da shakka cikin al’amarin su. Sun zo mashi da zuciyar kura amma sun lulluba da fatun raguna. Haka suka yi ta kwararo masa xaruruwan ruwayoyi na qarya masu nuna wai zaluncin da Sahabbai suka yi wa Iyalan Gidan Annabi (SAW). Saboda haka suka sanyawa wannan mutum shakka cikin masuluncin gaba xaya har ma ya yi burin da dai uwarsa ba ta haife shi ba, saboda haka ya kawo mani koken ruxun da ya shiga ya na mai neman a tantance masa haqiqanin gaskiya, a rabe masa aya daga tsakuwa.

Saboda haka na sanar da shi tangaryar gaskiya a fili varo-varo, da gamsassun hujjoji qarara, cewa Ahlul Sunna su ne tangaryar ma’abuta Alkurani da Sunnah, masoya Sahabbai da Iyalan Gidan Annabi (SAW), tsarkaka kuma ahalin masulunci da imani da ihisani.

Na kuma karantar da shi fahimtar haqiqanin matsayin waxannan shaixanun a kan cewa su kafirai ne waxanda suka yi ridda. Lallai ilahirin malaman masulunci da masulmai sun zartar da hukuncin kafirci a kan su. Kuma haqiqa ba domin taqiyya da munafuncin su ba tare da baiyanar da savanin abin da yake zuciyar su to, da hatta da mata da yara da jarirai da zauna gari banza sun hukunta kafirci a kansu.

Kuma na sanar da shi cewa lallai addini irin na (shi’ah) ithna ashariyyah ya kwaxaitar da mabiyan sa da su tarkato masa duk wani nau’in kafirci da al’ummomin kafirai suka yi furuci da shi, da duk wani nau’ in shirka da al’ummomi matsafa mushirikai suka auka ciki, da duk wani nau’in wuce wuri da yahudu da nasara da makarkata suka auka ciki da dukkan wani nau’in kafirci da aka san mulhidai da zindiqai da shi da kuma duk wani vata da bidi’a da tatsuniyoyi da qungiyoyin vata na zamani ke furuci da shi. Sun tarkato irin munanan xabi’a da qeta na yahudawa, da nau’in vata da wuce wuri na nasara da gaba xayan aqidu na majusawa, da kuma taqiyya da munafunci iri na mulhidai. Haka sun kwaso ra’ ayoyin jahamiyya, da bidi’o’i irin na qadariyya (majusawan al’umma) da aqidoji da ra’ayoyin mu’tazilah da khawarijawa. Haka kuma na sanar da shi cewa haqiqa (shi’ah) imamiyya ithna ashariyya, mutane ne da babu wani da’awar vata da za’a yi face sun yi imani da shi kuma sun sakankance da faruwan shi, babu wani savo da mummunar xabi’a da ha’inci face sun lulluba da shi, babu wani ra’ayi da wuce iyaka face sun yi riqo da shi. Saboda haka su mabiya shaixanu ne kuma masu shaixanun mutane cikin su kuma cikakkun munafukai. Suna baiyana imani amma suna voye kafirci da zindiqanci. Suna kuma damfaran muminai masu tsaron Allah a kan addinin su. Suna riqo hannayen su su fitar da su daga imani zuwa kafirci, daga yakini zuwa ga shakka, daga kwanciyar hankali zuwa ruxu da vata. Ba mu da wani natsuwa dangane da su baya ga fadin Allah (swt): “Lallai ne, munafukai suna a magangara mafi kaskanci daga wuta. Kuma ba za ka sama masu mataimaki ba”. [Nisa’i:145]

Waxannan kalamai nawa sun sanyaya zafin ruxanin da ke gudana a jinin sahibi na. Natsuwar sa da masulunci ya sake dawowa tare da imanin sa da tsoron Allah sa. Sai muka yi bankwana ya na cikin natsuwa da aminci kuma ya na mai yarda da Sahabbai masu karimci.

Amma kashe gari sai ga shi ya dawo gare ni da saqon cewa : “Lallai waxannan mutanen (shia) sun taru yanzun haka suna sauraren zuwan ka saboda sun zartar da shawaran yin muqabala da kai. Saboda haka sai ka yi azama ka shirya hujjoji kuma ka yi tawakkali ga Allah domin da Allah ne masu tawakkali suke dogaro” sai na ce da shi: “Wannan mutane fa son rai ya yi masu kanta mutuqar tuqewa don haka babu yadda za su saurari gaskiya daga wani mutun.” Babu wanda ya fi su qarya a bayan qasa. Sun riqi qarya a matsayin addinin da ibada da hanyar samun kusanci da lada. Saboda haka duk lokacin da wasu mutane suka baiwa qarya irin wannan matsayi to, ba fa za su saurari gaskiya ba, in kuma ma sun ji ba za su yi anfani da shi ba.

Kuma fa ka sani su mayaudara ne masu baiyana savanin abinda suka voye, saboda haka kada ka yi tsammani akwai wata fa’ida da za ka yi kwaxayin samu in mun yi muqabala da su.

Bugu da qari kuma su mutane ne da ba su da hankali balle su wa’aztu kuma su yi tunani. Babu wani sahihin zance da za mu kawo mu kafa masu hujja su yarda. Kuma ka sani su suna rayuwan addinin su ne a kan motsa kishi na qarya da yaudara da vata wanda duk Ibilis la’ananne ke harraka shi. Shi kuwa abin sani dai kishi da hamasa irin na jahiliyya a wajen kafirai kaxai aka san shi. Ai hankali da duk wani addini sahihi ba ya karvan canfi da tatsuniyoyi (a matsayin hujja). Alhali su ire iren waxannan canfe canfe da tatsuniyoyi da motsa kishi na son rai, suke girmawawa suna fatawa da su. Saboda haka ina anfanin tattaunawa da yin muqabala da su.

Amma duk da wannan bayanan ban iya gamsar da sahibi na ba. Haka dai wannan muqabalar ta auko mani kwatsam kuma na tafi da matuqar kwaxayin isar da sako. Haqiqa maqabalar muqaddari ne a gare ni daga Allah. Kuma haqiqa muqabalar ta tsawaita har sai da ta game duk inda ake da savani, ta zarce har zuwa kwanaki biyu a jere daga bayan sallar Isha’ zuwa sallar Alfijir a kowace rana. Kuma alhamdu lillah, haqiqa na samu muwafaqa bisa falala da baiwa daga Allah. Alhamdu lillah bisa ga taimako da sauqaqewar Allah shi kaxai, na samu sauqi qwarai wajen tsage gaskiya har ta kai a qarshen mukabalar, sahibi na ya xaga murya ya ce: “Godiya ta tabbata ga Allah da Ya baiyanar da gaskiya, godiya ta tabbata ga Allah da Ya baiyanar da gaskiya!! Haqiqa yau duniya ta zama sabuwa a gare ni. Na xanxani zaqin gaskiya. Godiya ga Allah da ya xaukaka gaskiya ta harshen ka”

Su kuma sun kasance qasqantattu suna ma su sallamawa, kawunan su a duqe bayan sun sha ruwan hujjoji na gaskiya. Kuma godiya ga Allah da ya rinjayar da gaskiya ya baiyanar da hujojji domin wanda zai halaka a cikin mahalarta ya halaka da hujja kuma wanda zai shiryu cikin mahalartan ya shiryu a bisa hujja. Godiya ga Allah tun daga farko har zuwa karshe.

Na yi azamar yin rubutu a kan wancan arangamar na haqiqa da hujjoji bayyanannu domin kwaxayin yaxa ilimi da fa’idantar da masulmai, da faxakar da waxanda suka gafala da irin haxarin waxancan mutanen da gargadi a kan yin abota da su da rufe bakin masu yekuwar samun fahintar juna da haxa kai da waxannan mutane, da shelantawa malamai bayin Allah su gane haqiqanin waxannan mutane da irin abin da suka ginu akai na kafirci da shirka da bidi’a da vata da jahilci da canfi da qarya da yaudara da munafunci da ha’inci da kafirci.
Ina rokon Allah (SWT) Ya sa wannan ya zama nasiha da fa’ida ga masulmai, kuma ya zama sanadin wayar da kan al’umma su fahimci haqiqanin maqiyan su, mayaudara kuma makirai.

Kuma ina kwaxayin samun sakaiya daga Allah ne Shi kaxai, Ya wadace mu kuma madalla da abin dogaro. Godiya ya tabbata ga Allah Ubangijin dukkan halitta.
Majdi Muhammad bn Ali bn Muhammad

FASALI NA XAYA
Muqabala ta farko
Gabatarwa

A shafuka da ke tafe za’a karanta yadda muqabala ta gudana tsakani na da wani daga cikin malaman Shi’a Immamiya Ithna ashariyyah wannan kuma ya faru ne bisa wata qaddara daga Allah ba tare da wani tsari daga gare ni ba. Haka Allah Ya so al’amarin ya faru domin gaskiya ta baiyana quru-quru a sarari, musammam ga waxansu mabiya Sunnah da aka yaudara da da’awar da wasu cibiyoyin shi’a suke yi na iqirarin haxin kai a addinance amma a bayan fage suna yaxa aqidun shi’a a tsakanin matasan Ahlul Sunnah wanxanda suke da raunin ilimin tangaryar gaskiya.

Burin su kullum shi ne cusawa matasa shakka a Alkur’ani da hadisi bayan yaqinin da suke da shi, su musanya yaqinin da suke da shi a kan jagorori na qwarai, Sahabban Annabi (SAW) waxanda Allah Ya rene su bisa kulawarSa kuma Annabi (SAW) ya tsarkake da ayoyin Alkur’ani da hadisai, har su kai fagen koya masu zagin Sahabban da tsine masu da kafirta su. Kazalika suna halasta jini da dukiyar masulmai da keta dukkan haddinsa, a maimakon aminci da walwala da yake da shi. Kuma burin su ne fitar da su daga gaskiya zuwa ga qarya, daga shiriya zuwa ga vata, ta hanyar munanan makirci da yaudara.

Amma ta Allah ba ta su ba, har abada gaskiya ba za ta rushe qarya ta yi rinjaye ba, domin Allah ta’ala Ya ce: “Kuma ka ce, “Gaskiya ta zo, kuma qarya ta lalace. Lalle ne qarya ta kasance lalatacciya.” (Isra’:81)

Lallai wannan muqabala ta tsawaita har sai da ta game mafi yawaicin wuraren da ake da savani tsakanin mabiya gaskiya tsantsa, watau Ahalul Sunnah wal jamaa, da ma’abuta qarya mabiya vata, kuma masu watsi da gaskiya: a karshe gaskiya ta baiyana varo-varo har sai da wani cikin waxanda aka yaudara ya yi yekuwa da babban murya ya na mai fadin cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah da Ya baiyanar da gaskiya, godiya ta tabbata ga Allah da Ya baiyanar da gaskiya. Yau na fahimci gaskiya kuma na shiga wata sabuwar rayuwa. Godiya ga Allah da Ya xaukaka gaskiya ta harshen ka.” Sun kuma kasance qasqantu, wulaqantattu. Godiya ga Allah da Ya baiyanar da gaskiya domin wanda duk zai halaka to ya halaka da hujja, kuma wanda zai shiryu to ya shiryu a kan hujja.
DALILIN MUQABALAR

Ni ina da cikakken gamsuwa cewa yin jidali da ‘yan shi’a, magoya bayan qarya, ba zai haifar da xa mai ido ba domin babu shakka su ne mafiya qarya duka a cikin mutane. Sun mayar da yin qarya addini kuma cikon ‘ibadar’ samun kusanci ga Allah. Yin jidali da mutanen da suke da irin wannan halaiya ba shi da wani anfani. Domin mai irin wannan hali zai riqa fadin abin da yake savanin zuciyarsa, ya yi ta kwana-kwana wajen magana, ga yaudara in ya sami kafa, sannan in aka yi galaba a kan shi sai ya nuna kamar ya miqa wuya alhali kuwa qarya yake yi. Don haka babu wata fa’ida ko alheri na tataunawa da su.

Kuma son rai ya rinjaye su matuqa da gaske ta yadda zai wuyata su saurari gaskiya ko yin kyakkyawar tunani akai.

Bugu da kari kuma, su mutane ne da ba su anfani da hankali ko nassi. In ka zanta da su bisa anfani da hankali ba za su hankalta su fahinta ba. Suna rayuwa ne a kan motsa kishi na yaudara da canfe-canfe na jahilci wanda hankali da addini ba za su karve su ba, illa dai kasancewar ta wata fitine da suke girmawawa. In kuwa ka naqalto masu wani hadisi sai ka ga sun fi kowa nisanta da jahiltan shi. Sigar duk hadisan su shi ne: “kaka na ya bani labari, daga Jibirilu”, ko kuma, “zuciya ta ta bani labari daga Ubangiji na.” Wannan dalilai da ire-iren su ne ya sa mani sakankancewar rashin anfanin tattaunawa da waxannan mutanen.

Muqabalar ta faxo mani ne bisa qaddara ba tare da na tsammaci zuwan ta ba.

Akwai wani matashi mai cikakkiyar dabi’ah da kyawawan halaye, wanda damqar qazamar hannun ‘yan shi’a ta kai ga zuciya da hankalin shi, su ka shige shi saboda qarancin ilimin shi har suka ci nasaran yaqan lafiyaiya kuma tsarkakakkiyar aqidar shi ta hanyar makircin su da yaudara watau sun nuna mashi tsananin so da qauna da matukar karamci har sai da ya zaci kamar sun zarce kowa kyawawan davi’u da riko da addini. Yayin da suka ga ya shaku da su sai suka shiga yi masa bayanin Iyalan Gidan Annabi (SAW), (Ahlul baiti) mafiya tsarkin tsarkaka, da nuna cewa su ne, tun tsawon tarihin masulunci, magoya bayan Ahlul Baiti, waxanda aka zalunta. Kuma cewa su ne mabiya Imam Ali (RA), xan’uwan Annabi (SAW), wanda kuma matsayin sa(a wajen Annabi) kamar na Haruna ne a wajen Musa (AS) domin Annabi ya na son shi ya kuma sa a so shi yayin da ya ce: “Ya Ubangiji ka so wanda ya so shi kuma ka qi wanda ya qi shi.” Da kuma cewa su ne masoya Al-Hassan da Al-Hussain shugabannin matsan ‘yan Aljanna kuma mahaifiyar su ita ce shugabar matan Aljanna da dai sauransu. Har ta kai dai wannan bawan Allah ya zaci kamar dai su waxansu mala’ikun rahma ne Allah ya aiko domin su shiryar da shi. Bari in qyale ku ji bayani daga gare shi irin halin da ya shiga domin waqa dai a bakin mai ita ta fi daxi.


BAYANIN MATASHIN DA YA SHIGA RUXU DA MUSABBABIN SHIGA RUXUN
Wani matashi mai kyakkyawar xabi’a ya zo gare ni, a saduwarmu da shi na farko, ya ce da ni, “Wane, haqiqa fa ni na shiga cikin wani hali na rudu mai tsanani har ya kai ina burin da ma tun farko uwata ba ta haife ni ba kuma da ma ba’a tava yi na ba a doron qasa.” Sai na ce da shi, “ka kwantar da hankalin ka domin rahmar Allah mai yalwa ta ishi komai kuma ba shakka an umarce mu da kada mu yanke tsammani ga rahmar Allah ta’ala.” Haka dai na yi ta rarrashi da kwantar masa da hankali domin duk da ban san haqiqanin mai ya same shi ba, na fahimci ya na cikin wani mawuyacin hali mai tsanani.
Sai ya ce da ni, “Wane! Naji kalmomi na alheri daga gare ka. Ni na zo ne wajen ka domin sanin kurakurai na. Ina kuma ganin kai nakwarai ne, amma Allah ne mafi sani. Kuma ba zan tsarkake wani a wajen Allah ba.”
Na ce da shi, “Insha Allah ina sauraren ka. Ka ci gaba ka amayar da duka abin da yake damun ka, in kuma Allah Ya so za ka samu amsar ruxun da kake ciki.”
Sai matashin ya ce, “Tun wani lokaci da ya gabata na sadu da wani matashi xan shi’a wanda muka yi ta mu’amala tare har muka shaku da juna sosai. Yana yawaita yin mani bayani a kan Iyalan Gidan Annabi (SAW) har ta kai lokacin da na yi zurfi qwarai cikin soyaiya ga su Iyalan Gidan Al-Mustafa (SAW). Kuma wannan ba abin mamaki ba ne tun da dai haka aka buqaci ko wanne musulmi ya zama masoyin su bisa koyi da faxin Allah ta’ala: “Ka ce, “Ba ni tambayar ku wata ijara a kansa face dai soyaiya a cikin zumunta.”(Shura:23); da kuma koyin da fadin Annabi (SAW): “Ba xayan ku da zai yi imani har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi fiye da iyayen shi, da ‘ya’yan shi da sauran mutane baki xaya”. Kuma dai shakka babu dangin Annabi (SAW) sun fi soyuwa ga mumini fiye da dangin sa.”

“Alaqa ta da wannan matashi xan shi’a ya qara kore mani duk abinda aka san ‘yan shi’a da shi na cewa su ‘yan bidi’a ne vatattu. Kawai sai qara samun kusanci ya ke yi gare ni. Kusancin a gare ni ya xauki wani salo na musamman har ta kai zai zo da motar sa don ya yi mani hidima. Al’amarin ya kai har sai da ya ribace ni da irin karamcin sa a gare ni, wanda haka kuma ya gaskata faxin wani mawaki cewa;

“In ka girmama (mutum) abin girmamawa sai ka mallake shi”.

“Ana nan kuma sai ya shiga ba ni labarin wasu aqidoji kyawawa wanda can baya na zaci ‘yan shia sam ba su yarda da su ba. Ya kan gaya mani irin yadda shi da duk ‘yan shi’a ke son Annabi (SAW), da irin son sa da na ilahirin shi’a ga Iyalan Gidan Annabi (SAW)’ irin su Fatimat al Zahra’u’ ‘yar Manzon Allah (SAW) wadda Annabi ya ce don gane da ita’, “ku saurara, haqiqa Fatima tsoka ce daga gare ni. Wanda duk ya cutar da ita to, ya cutar da ni, wanda kuma ya cutar da ni ya savi Allah (Azza wa jalla)”; kuma ita ce shugabar matan Aljannah; da kuma irin son da ya ke yiwa Al Hassan da Al Hussein, shugabannin samarin Al jannah; da soyayyar shi da na ilahirin shi’a ga Imam Ali xan’uwan Manzon Allah (SAW), kuma surukin shi,masoyin shi.

Dukkan wadannan abubuwa babu wata damuwa a kan su domin tun daga birnin zuciya ta na san haka suke kuma ina girmama su. Kuma har na kan ce ma shi “Ai mu ma muna son duk waxannan (Ahlulbaiti) gaba xayan su”, amma sai gogan ya qi tanka mani. Koda yake (shirun) na dan wani lokaci ne kawai”.

Alaqa tsakanin na da shi ya qarfafa har ya kan kai ni wajen abokan shi waxanda duk tafiyar su xaya ce.Waxannan masu kyawawan xabi’u suna ji da ni qwarai har ta kai ina jin kamar dai ba mutane ba ne face wasu mala’iku ne a bayan qasa. Idan ina da wata buqata nan take zan samu, in kuma ina da burin tafiya wani wuri sai gaba xayan su, su xunguma domin su kai ni. Haka dai mu ka kasance har wata rana suka ba ni wani littafi mai kyau wanda a ciki ban ga wani illa na shi’anci a ciki ba. Ban gushe ba ina tunanin wannan littafin da ya sa ni zurfin tafakkuri a kan shi’anci. Sunan littafin, “Ahlulbaiti: Maqamahum, Manhajuhum, Masarihim” (Ahlul baiti: Matsayinsu, Manhajar su da Tarihin su).

Wannan littafi na cike da Hadisai da Ahlul Sunnah suka aminta da su waxanda ke kira ga soyayya da jivinta da yabon su Ahlul baiti. Kuma wani lokaci sai in ji na karkata ga Akidar da suka ginu akai. Na kan shiga halin tufka da warwara tare da shakka da kan faxo mani cikin zuciya ta. Shi dai wannan littafi yana nuna cewa su shi’ah sun yi imani da Alqur’ani da hadisai, su na girmama Ahlul baiti, wanda kuma duka su ne ababen da ake nema daga kowanne musulmi, mumini mai kaxaita Allah.

Daga nan fa sai wancan abokin nawa ya fara bayyana mani aqidar shi ta shi’ah da ababen da aka yaudare ni cikin su.

A lokutan baya na kan ji a na cewa ita mazhaba ce karkatacciya ta vata, wadda ta xoru a kan zagi da la’ana da kafirta Sahabbai, da qiyayya ga Ahalul Sunnah wal jama’a da yin canje-canje a Alkurani, amma sai ga littafan su na kore wannan gaba xaya. Haka dai ya yi ta koro mani bayanan shi’anci xaya bayan xaya.

Har wayau ya bani wani littafi da ba zan manta sunan shi ba, watau ‘Almuraji’at’. Na karkata zuwa ga wannan littafi qwarai, ina karanta shi ina maimaitawa kuma ina mamakin wannan babban shehin malami (da labarin sa yazo a littafin) watau babban shehi na Jami’ar Azhar wanda aka rubuta cewa ya sallama ga dukkan hujjojin da wani matashin xan shi’a ya gabatar ma sa a wancan lokacin. Wannan matashi shine Abdul Hussain Sharafuddeen Al Musawi!!

Na yi farin cikin samun wannan littafi kuma ma har na kan ce, to mene ne Ahlul Sunnah wal jama’a za su ce a kan wannan littafi? Wannan ya sa har na ke ganin samun haxin kai tsakanin mu da shi’a kusa yake in ba domin jahilcin maluman mu ba a kan sanin haqiqanin mene ne shia. Wannan abokin nawa ya taimake ni samun fahimtar cewa cikkaken haxin kan masulmai zai samu ne idan duk Ahalul sunnah suka rungumi shi’a ta yadda baki xaya za mu shiga jirgin tsira, watau jirgin Annabi (SAW) da Iyalan shi ma su girma kuma tsarkaka.

Kada dai in tsawaita maka labari. Haka na kasance cikin wannan hali tsawon watani hudu ina qara shakuwa da xan’uwa na xan shi’a har ta kai ina bin shi zuwa cibiyoyin karatuttukan su. Kaico na! Ina ma dai da ban je ba!!

Wataqila za ka yi mamaki (fadin haka da na yi)! Haka batun yake. Kaico na, ina ma dai da ban je ba! Ni dai na saba duk lokacin da na ji an ambaci sunan Abubakar ko Umar zan ce Allah ya yarda da su. Wannan kuwa saboda shi Abubakar shi ne Assiddiqu wanda ke tare da Annabi (SAW) a cikin kogo, kuma a masulunci shi ne ‘xayan mutum biyu’. Har wayau shi ne mahaifin Uwar Muminai, A’ishatu Assiddiqatu. Kuma bugu da qari shi ne khalifan masulmai; sannan ga Umar Al Faruq, mai rabewa ta kanin gaskiya da karya, kuma shi ne dai wanda Allah (SWT) ya qarfafa masulunci da shi aka yi buxin qasashe ta hannun shi, kuma shi ne khalifan masulmai, adalin shugaba, kuma Amirul Muminina. Wannan shi ne matsayin aqida ta game da su biyun nan.

To, a farko-farkon al’amari su (‘yan shi’a) sun xan daure (suka kau da kai) game da wannan matsayin nawa. Sai dai so da yawa wannan abokin nawa ya kan kawo mani labarin irin zaluncin da aka yiwa Imam Ali (RA) da yadda aka qwace ma shi haqin shi na wilaya da jagoranci, amma duk wannan bai tava sa na girgiza ba sai wata rana da wani abu ya faru kamar haka.

Na kasance tare da su wata rana sai aka ambaci sunan Umar Al Faruq, sai na ce “Allah ya yarda da shi”. Kwatsam sai wani daga cikin su ya kwave ni, ya ce: “wannan kafiri ne, murtaddi, tsinanne, kada ka nema ma shi yardan Allah. Alal haqiqa wannan kalamai na shi sun zo mani kamar wata tsawa daga sama. Domin shin mene matsayin shi da kuma (abin da yake cikin) littafan su waxanda aka yi ta bijiro mani da su, wadanda ko kusa ba su ambaci Sahabbai da wani mummunan abu ba? Saboda haka nace: “Kila dai wannan irin mutanen nan ne masu tsananin ra’ayi da wuce wuri”. Amma da sannu sai na ga ashe dukkan su haka suke, matsayi da ra’ayin su xaya ne.

Kuma sai wannan abokin nawa ya faiyace mani gaskiya cewa: “Lallai aqidar mu ta kafu ne a kan al’wila’u da al’bara’u. Al-wila’u shi ne son Ahlul Baiti tsarkaka, alhali al bara’u na nufin qiyayya da waxanda su ka yi adawa da su kuma su ka qwace ma su haqqin su”.

Haka dai ya yi ta ba ni labarun yadda wai Abubakar da Umar suka riqa zaluntar Ahlul Baiti da wulaqanta Ali da qona gidan shi da na Fatima, da dukan ta a ciki har ta yi varin ciki, kuma wai wannan raunin shi ya yi sanadiyar rasuwan ta. Labaru dai na baqin ciki da takaici waxanda aikata su yake tare da qasqanci, amma kuma wai duk Abubakar da Umar suka aikata.

Kuma maganar gaskiya babu voyo duk wasu alamun sunnah a waje na tuni sun vace vat. Kawai sai na dulmiya tare da su ina gaskata dukkan irin waxannan ruwayoyin da suke kawowa don gane da Abubakar da Umar (RA) har qiyayya da su ya kurxa cikin zuciya ta. Haqiqa, qiyayya da su ya kurxa cikin zuciya ta, Musamman yayin da na ke sauraron qissar ranar Raziyya1. Ta yaya Umar zai tsaya ya dubi fuskar Annabi (SAW) ya hana shi rubuta wannan wasiyya?!!.

Kuma cikin xan lokaci kaxan na samu mumunar qulli a zuciya ta game da Sahabbai saboda yawaitan sauraron qissosin zaluncin da aka ce sun yiwa Imam Ali da Iyalan Gidan shi. Kazalika ina qin duk wani da ba xan shi’a ba ne a dalilin yawan jin labarun zaluncin da aka ce an yiwa sauran Ahlul Baiti na vangaren Iyalan Imam Ali, musamman qisar Al Hussain (RA).

Haka dai na zama xan shi’a, ciki da waje. Abubuwan da a lokutan baya ba shi yiyuwa in gaskata, amma sai ga shi duk ina gaskatawa daga gare su. Kamar misalin cewa wai dukkan Sahabbai sun kafirta in ban da Miqidadu da Abu Zarri da Salman da Ammar da mabiya Ali, da cewa addini ya ginu ne a kan yin bara’a gare su (Sahabbai). Qwarai, don me haka ba zai kasance ba, alhali sun qwace wa Ahlul baiti haqqin su. Saboda haka addini ba zai ginu ba sai a kan asasin zagin su, da la’anar su, da jifan su da munanan tsinuwa da zagi.

Sai dai fa duk da haka zuciya ta bata yarda da wannan zage-zagen ba domin ya na sosa mani rai. A saboda haka in ina tare da su zantukan su ya kan yi tasiri a gare ni tare da cewa ilahirin su kissosi ne masu motsa kishi a kan zaluntar su Ali (RA) da kisan Al-Hussain (RA). A taqaice dai kissosin ne da ake yawaita anbaton su, waxanda kuma suke iya motsa mutun zuwa ga yin hushi da qiyayya da waxanda suka zalunci Ahlul Baiti da maciya haqqoqin su.

Amma duk lokacin da na kaxaita sai zuciya ta ta ce yaya zaka aminta da zagin Abubakar wanda a kowace lokaci ya na tare da Annabi (SAW)? Yaya zaka aminta da zagin Umar wanda gaskiya ke fita ta harshen shi? Yaya zaka aminta da zagin Uthmanu wanda ya tattara Alkur’ani ya rubuce shi ya kare shi daga gurvacewa da kuma savani? Yaya zaka aminta da zagin duk wani Sahabin Annabi (SAW)? Shin idan ka zazzage su, me kuma ya yi saura maka a masulunci?

Wallahi wanna ruxani ne mai girman gaske (nake ciki) wanda Allah kaxai ya san irin girma da faxin shi. A halin yanzu ma ina maka wanan magana ne tare da burin da ma dai uwata bata haife ni ba, ko kuma da dai tuni na mutu kafin yanzu an manta da ni kwata-kwata!!”

A nan sai ya xaga kai ya kalle ni ya ce: “Wane! Haqiqa ina cikin ruxu. Na zama jemage, ni ba Sunni ba, ba kuma Shi’a ba. Aqida ta ta Sunnah da na taso ciki, tsawon rayuwa ta, tana fizga na, sannan ta xaya vangaren shi’ancin da na shiga na fizga na a xaya gefen. Duk lokacin da nake tare da waxannan mutane sai in karkata ga shi’anci duk da haxarin da ke tare da shi na zagi da la’ana ga waxanda ba su cancanci la’anar ba. Amma idan na kaxaita da kaina sai in ji na karkata ga aqidar Sunnah da aminci, watau soyayya da yarda da Ahlul baiti da Sahabbai gaba xayan su.

Shin ya kai wane, ko ka na da magani da waraka ga irin ruxu da shakku da na ke ciki, tare da wasu hujjojin masu warkarwa ga irin halin da nake ciki? Ina neman izinin ka bisa cewa tattaunawa na da kai ya kasance ta mahangan shi’ah ne tsantsa zai gudana in har ka yi niyyar yin muqabala da ni. Kuma kada ka munana zato a gare ni domin ni ina farautan inda gaskiya take ne koda kuwa ta kowannan irin hali ko fuska za ta kasance”.

  1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©anasahife.org 2016
rəhbərliyinə müraciət